Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: A martanin da ta mayar, Hamas ta amince da sakin fursunonin da suke raye da kuma mika gawarwakin fursunonin Isra'ila da suka mutu a madadin sakin fursunonin Falasdinu masu yawa, amma ta bayyana cewa " kwance damarar gwagwarmaya" zai kasance ne da sharadi kawo karshen ayyukan mamayar Isr’aila kuma "nau'in gwamnati mai zuwa a Gaza" ta kasance karkashin ra'ayin jama'a da bangarorin gaba daya.
Hamas ta kuma bayyana karara, sabanin bukatar Trump da Netanyahu na ganin rushewar gwagwarmaya, cewa kungiyar za ta shiga cikin harkokin gudanarwar Gaza a nan gaba a matsayin wani bangare na tsarin kasa, tare da cikakken alhakinta.
Duk da wannan ababen lura, shugaban na Amurka ya matsa wa gwamnatin sahyoniyawan kisan kiyashin yara kan su dakatar da aikin soji a Gaza.
Wasu kafafen yada labaran Amurka sun ruwaito daga wani babban jami’in Isra’ila, cewa Netanyahu ya kadu da martanin da Trump ya yi kan martanin Hamas. Ya dauki abin da ke cikin martanin Hamas a matsayin "kin amincewa da shirin Trump" kuma ya yi kira da a hada kai da Washington don hana samun kyakkyawar fahimtar matsayin Hamas.
Your Comment